Corona ta bulla a Afganistan

A karon farko an samu bullar cutar Corona (Convid-19) a yammacin kasar Afganistan.

1365131
Corona ta bulla a Afganistan

A karon farko an samu bullar cutar Corona (Convid-19) a yammacin kasar Afganistan.

Ministan Kula da Lafiyar Al'uma Ferozuddin Feroz ya fadi cewar an samu wani mutum 1 dauke da cutar a jihar Herat dake yammacin kasar.

Feroz ya ce an sanar da dokar ta baci a jihar.

A gefe guda kuma an tsare mutane 10 da ake zargin suna dauke da cutar ta corona a kasar.

Cutar corona da ta bullo daga jihar Hubey ta China ta kama mutane dubu 79 a duniya baki daya.

Mutane dubu 2,594 cutar ta kashe a cikin kasar China.Labarai masu alaka