Kafa tarihin yawon shakatawa zuwa sararin samaniya

Kamfanin SpaceX da kamfanin yawon shakatawa na sararin samaniya, Space Adventures sun bayar da sanarwar cewa za su fara zirga-zirgar jiragen sama wadanda za su kawo masu yawon shakatawa zuwa sararin samaniya a shekara mai zuwa.

1362761

Masu yawon bude ido za su yi wannan tafiya tare da jirgin saman sararin samaniya mai suna "Crew Dragon".

Shugaban Kamfanin SpaceX, Gwynne Shotwell ya yi magana kan aikinsu tare da Space Adventures inda ya bayyana cewar,

"Wannan manufa ta tarihi za ta samar da wata hanyar da za ta bayar da damar samar da sararin samaniya ga dukkan mutanen da suke fata. Muna farin ciki da yin wannan aikin tare da Space Adventures." 

Space Adventures wanda aka kafa a shekarar 1998, zai zama mai kula da daidaitawar fararen hula da suke son tafiya cikin sararin samaniya a cikin wannan aikin tare da SpaceX.

Ya zuwa yanzu kamfanin ya tura 'yan yawon bude ido 7 zuwa sama da kumbon Soyuz na Rasha dake tashar sararin samaniya ta Kasa (ISS).

A karo na gaba kan balaguron sararin samaniya, fasinjoji zasu hada da wanda ya kirkiro Microsoft, Charles Simonyi da kuma mace ta farko da za ta je yawon shakatawa zuwa sararin samaniya, wata mai arziki 'yar kasar Iran, Anousheh Ansari.

Duk da yake ana tsammanin jirgin saman na Crew Dragon ya tashi sama a duniya ba tare da tsayawa ISS ba, SpaceX zai sami damar kara yawan fasinjojin da za su kasance a cikin kewayen duniya, har zuwa 4 fiye da yadda aka taba gani.

 Labarai masu alaka