Ta yaya kasashen Afirka za su yaki cutar Corona

A watan Disamban shekarar da ta gabata ne annobar Corona ta bulla a wata kasuwa dake garin Wuhan na kasar China wanda hakan ya sanya Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ayyana dokar ta baci a bangaren kula da lafiya a matakin kasa da kasa.

Ta yaya kasashen Afirka za su yaki cutar Corona

A watan Disamban shekarar da ta gabata ne annobar Corona ta bulla a wata kasuwa dake garin Wuhan na kasar China wanda hakan ya sanya Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ayyana dokar ta baci a bangaren kula da lafiya a matakin kasa da kasa. Bayanan da mahukuntan China suka fitar na karshe na cewar sama da mutane dubu daya cutar corona ta kashe a kasar. Wadanda ta kama kuma sun haura dubu 42,200. Baya ga asalin kasar China, a yankunan Filisins da Hong Kong ma an samu bullar cutar inda mutane 2 suka mutu a Hong Kong, kuma a kasashe 24 ma an samu masu dauke da ita.

Mai bincike Ibrahim Bachir Abdoulaye (Dalibin digirgir a jami’ar Bayreuth) ne ya yi mana sharihi kan wannan batu.

Ya zuwa yanzu ba a samu bullar cutar Corona a wata kasa dake Afirka ba amma duk da hakan ana fargabar afkuwarta saboda yadda Afirka ta zama babbar kawar China a fannin kasuwanci. Musamman yadda kasashen Afirka ba su da manyan kayan kimiyya da fasaha don yaki da cutar, hakan na kara karfafa fargabar da ake da ita.

Wannan alaka mai karfi ta kasuwanci na kara karfafa tsakanin China da nahiyar Afirka. Akwai kusan ‘yan kasar China miliyan 1 da suke rayuwa a Afirka dake da mutane biliyan 1.2. Kuma ‘Yan China dubu 10,00 ne suke harkokin kasuwanci daga cikinsu. A gefe guda, akwai ‘yan Afirka sama da dubu 80,000 dake karatu a China kuma daga cikinsu akwai dubu 5,000 da suke a garin Wuhan.

Kamar yadda yake a sauran kasashe, a kasashen Afirka ma an daki matakan hana zuwa China don magance yaduwar cutar. Duk da yadda wasu kasashen suke da yawan maziyarta daga ko zuwa China, hakan bai hana su daukar matakan da suka kamata ba.

Misali jiragen saman kasashen Kenya, Ruanda, Morokko, Masar, Madagascar, Mauritius da Tazania sun dakatar da zuwa China. Wasu kasashen kuma sun dakatar da ba wa ‘yan kasar China Visa. Misalin Mozambique, ta sanar da dakatar da bayar da Visa a kan iyakokinta ga ‘yan kasar China. Haka zalika Koriya ta Kudu ta dauki matakai game da kayan da ake kawowa daga China. Amma kuma kamfanin jiragen sama mafi girma a nahiyar na Etheopea Airlines na ci gaba da zuwa China. Mahukuntan Ethiopea na cewa duk wadanda suka zo daga China ana killace su. Wasu na cewar a kowacce rana mutane dubu 1,500 ne suke zuwa Afirka daga China don kauwanci ko yawon bude ido.

China na kokarin magance matsalar da za ta iya zuwa tsakaninta da Afirka wajen kasuwanci saboda corona. Hakan ya sanya mahukuntan China dake kasashen Afirka suke bayar da bayanai kan irin matakan da China ke dauka don hana cutar yaduwa. Sannan ta hanyar gudanar da taron manema labarai, kafafafan yada labarai na Afirka na yada irin kokarin da Chinan ke yi don hana yaduwar cutar . A karkashin hakan a wata sanarwar da jakadan China a Afirka ta Kudu ya yi ya fadi cewar babu bukatar ‘yan Afirka su firgita game da cutar corona. A ‘yan kwanakin nan corona ta janyowa China bakn jini. Hakan ya sanya China ke amfani da kafafan yada labarai da hanyoyin diplomasiyya don magance matsalar. Tare da hakan kasashen Afirka sun bayar da snaarwar syna tare da China a wannan hali da ta samu kanta a ciki. Misal Equitorial Guinea ta sanar da za ta bayar da taimakon dala miliyan 2 ga China don yaki da cutar corona.

Duk da matakan riga-kafi da aka dauka a Afirka hatsarinta na karuwa

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta dubba yadda ake awan zuwa Afirka daga China inda ta ce hatsarin bullar cutar ya fi yawa a kasashen Afirka da suka hada da Aljeriya, Angola, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Itopiya, Gana, Ivory Coast, Kenya, Mauritius, Najeriya, Afirka ta Kudu, Tanzania, Uganda da Zambia.

Sakamakon yadda a Afirka babu kayan kula da lafiya ingantattu da dakunan bincike masu kyau ya sanya alke ganin da wahala a iya gano cutar da wuri sannan a magance ta kafin ta yadu. Musamman a kasashe matalauta da ba su da komai hakan abu ne mai matukar wahala. Tare da hakan akasashen Sanagal da Afirka ta Kudu an ajje na’urorin iya gano cutar corona. Amma kuma kasashen Gana, najeriya, Madagascar da Saliyo sun bayyana cewar suna da kayan aikin gwajin cutar tare da magance ta. Amma fa babu dakunan bincike isassu a nahiyar. A watan Janairu domin yin gwaji kan wani mutum a Ivroy Coast ko yana da corona, sai da aka aike da jininsa wani dakin bncike dake Faransa. Duk dakarancin kayan aiki amma kasashen Afirka na bayyana cewar za su iya yaki da cutar. Zambia dake daya daga cikin kasashen da China ta fi aiki a ciki a Afirka ta dauki kwararan matakai a yankunan da ‘yan kasar China suka fi zama.

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO da ta ayyana dokar ta baci game da corona a duniya ta fitar da wasu shirye-shirye don taimakawa kasashe matalauta da za a iya samun bullar cutar. WHO ta fara wani gangami na tara dala miliyan 675 don hana cutar yaduwa. A karkashin hakan tana shirin samar da magunguna ga kasashen Afika da dama.


Tag: Afirka , Corona

Labarai masu alaka