Zumrut na ziyara a Zambia

Ministar Jin Dadin Iyali, Kwadago da Hidimtawa Al'uma ta Turkiyya Zehra Zumrut Selcuk ta gana da Ministar Daidaiton Jinsi ta Zambia Elizabeth Phiri.

Zumrut na ziyara a Zambia

Ministar Jin Dadin Iyali, Kwadago da Hidimtawa Al'uma ta Turkiyya Zehra Zumrut Selcuk ta gana da Ministar Daidaiton Jinsi ta Zambia Elizabeth Phiri.

Zehra Zumrut Selcuk ta je Zambia don halartar taron Kwamitin Kasuwancin Hadaka na Turkiyya da Zambia inda ta gana da Phiri.

A ganawar ta su, Minista Selcuk ta ce cin zarafin mata da auren wuri matsala ce da ke damun duniya baki daya.

Ta ce, gwamnatin Turkiyya na bayar da taimako ga mata tare da ilmantar da su kuma akwai bukatar kasashen 2 su sanya hannu kan yarjejeniyar habaka dangantakarsu.

A nata bangaren Phiri ta ce, Zambia na aiki tukuru wajen kawar da nuna wa mata wariya da kuma auren wuri, kuma a shirye suke da su hada kai da Turkiyya a wannan bangare.

Labarai masu alaka