Indiya ta samu nasarar harba tauraron dan adam na GSAT-30 zuwa duniyar sama

Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Indiya (ISRO) ta bayyana cewar an samu nasarar zaunar da tauraron dan adam samfurin GSAT-30 a bigirensa dake duniyar sama kamar yadda aka tsara da nufin kyautata amfani da talabijin da sadarwa.

Sanarwar da ISRO ta fitar ta ce an harba tauraron na GSAT-30 daga Faransa ta hanyar amfani da kumbon Guyana da mislain karfe 02.35 na ranar Juma'ar nan.

Sanarwar ta ce tauraron na da nauyin tan 3 da kilogram 357 kuma zai taimaka wajen kyautatuwar yada shirin talabijin da sadarwa a Indiya.

 Labarai masu alaka