Trump ya sanar da kakabawa Iran sabbin takunkuman tattalin arziki

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya sanar da saka sabbin takunkumai masu tsauri ga Iran sakamakon hare-haren da ta kai kan sansanoninsu dake Iraki.

A lokacinda yake jawabi a wajen wani taro da aka gudanar a White House, Trump ya tabo batun rikicin da suke yi da Iran.

Ya bayyana cewar suna da dalilai na gaskiya da suka sanya su kashe Janar Kasim Sulaimani.

Ya ce "Tuntuni ya kamata a ce an kashe Sulaimani. Kuskuren gwamnatin Obama ya sanya Iran ta samu kudade wanda take amfani da su wajen daukar nauyin ta'addanci. Mu mun kawo karshen wannan abu."

Trump ya fadi cewar hare-haren da aka kai wa sansanoninsu a Iraki ba za su tafi haka kawai ba tare da samun martani ba.

Shugaban na Amurka ya ce "Mun kakabawa Iran takunkumai. Na baya suna da tsauri amma na yanzu sun fi muni. Dazun nan na sanya hannun amincewa da takunkuman. Ma'aikatar Baitulmali za ta bayar da sanarwa."Labarai masu alaka