Harkokin noma na bunkasa tattalin arzikin Turkiyya

A shekarar 2019 da ta gabata Turkiyya ta fitar da busasshen kayan marmari mai suna "apricot" a Turance zuwa kasashen waje 110.

Harkokin noma na bunkasa tattalin arzikin Turkiyya

A shekarar 2019 da ta gabata Turkiyya ta fitar da busasshen kayan marmari mai suna "apricot" a Turance zuwa kasashen waje 110.

A Malatya da ake da bishiyun apricot miliyan 8 daga cikin miliyan 17 da ake da su a Turkiyya baki daya, na samar da abinci ga iyalai kimanin dubu 50.

Baya ka baklava din Antep da bauren Aydin, apricot ne kayan marmari na 2 ya karbu a kasuwannin Turai da ma sauran yankuna inda a bara aka kai shi zuwa kasashen duniya 110.

A shekarar da ta gabata kasashen da suka fi sayen apricot daga Turkiyya su ne Amurka, Faransa, Rasha, Jamus da Ingila.Labarai masu alaka