An kaddamar da aikin TurkStream

Rasha ta bayyana cewa za ta fara tura iskar gas zuwa Turai ta Turkiyya yayin kaddamar da aikin bututun iskar gas na TurkStream a Istanbul.

An kaddamar da aikin TurkStream
putin-erdogan Turkakim1.jpg
Türkakim acilis.jpg
putin Turkakim.jpg
putin-erdogan Turkakim.jpg
erdogan Turkakim.jpg

Rasha ta bayyana cewa za ta fara tura iskar gas zuwa Turai ta Turkiyya yayin kaddamar da aikin bututun iskar gas na TurkStream a Istanbul.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Shugaban Rasha Vladimir Putin, Shugaban Serbia Aleksandar Vucic da Firaministan Jamhuriyar Bulgariya Boyko Borisov sun halarci bukin kaddamar da aikin bututun iskar gas na TurkStream a babban dakin taro na Halic.

A yayin bukin wanda aka fara da gabatar da bidiyon tsarin TurkSteam, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa TurkStream babban aikin tarihi ne dangane da dangantakar bangarorin biyu da taswirar makamashi inda Rasha ta bayar da babban taimako.

Erdogan ya bayyana cewa sun samu nasarar kammala shinfida bututun iskar gas da aka tsara a cikin shekara guda wanda zai dauki iskar gas cubic mita biliyan 31.5 inda biliyan 15.75 zai taho Turkiyya kai tsaye ba tare da shiga wata kasa ba.

A nasa jawabin Putin ya bayyana cewa;

Akwai ayyukan tayar da zaune tsaye a wannan yankin amma Turkiyya da Rasha suna matukar nuna bambancin yanayi.

Bayan tattaunawar, an hade tashar iskar gas ta Russkaya da tashar iskar gas ta Kiyikoy kuma an buɗe wani bawul ɗin iskar gas a matsayin nuna fara hankada iskar gas.

 Labarai masu alaka