Sin ta kara iza wutar yakin fasaha dake tsakaninta da Amurka

Gwamnatin Kasar Sin ta yanke shawarar haramta wa ofishi da kungiyoyin gwamnatin kasar anfani da dukkan na'urorin kwamfuta da manhajojin da kirar kasashn waje ne.

Rahoton ya zo ne daga jaridar Financial Times inda rahoton ya ce gwamnati ta bada watanni 3 a kawar da dukkan manhaja da kwamfuta da ba kirar Sin ba ne. 

Kwararru sun bayyana cewa wannan babban taku ne a yakin fasaha dake guda tsakanin Amurka da Sin inda zartarwar da Sin ta yi na haramta kayan fasahar kasashen waje zai durkusar da kanfanin Amurka kamar Dell, HP da Microsoft. 

Yakin fasahar dai ya tabarbare ne tun lokacin da Amurka ta yi wa kanfanin Sin Huawei takunkumin tattalin arziki inda kanfanin Google, Intel da Qualcomm suka yanke alakarsu da Huawei a watan Mayu. 

Tag: Amurka , Sin

Labarai masu alaka