Filin jirgin Esenboga ya samu fasinjoji miliyan 12.7 a cikin watanni 11

A karshen watan Nuwamba na wannan shekarar, adadin fasinjojin da suka yi amfani da Filin jirgin saman Ankara, Esenboga ya kai miliyan 12 da dubu 719 da dari 565.

Darakta Janar na Hukumar Kula da Filin Jiragen Sama ta Kasa (DHMI) ya bayar da sanarwa kan kididdigar filin jirgin  Esenboga ta watan Nuwamba inda ya bayyana cewa an samu fasinjojin cikin gida dubu 876 da 964, fasinjojin kasa da kasa dubu 165 da 88 kuma jimlar fasinjoji sun haura miliyan 1 da dubu 42 da 52.

A watan Nuwamba a filin jirgin Esenboga zirga-zirgar tashi da saukar jiragen sama ya kasance sama da dubu 6 da dari 164, na kasa da kasa kuma ya kai 1406 da jimillar zirga-zirgar da ta kai adaddin dubu 7 da 570.

Zirga-zirgar motoci dauke da kayayyaki ta kai tan dubu 8 da 825.

Yawan fasinjojin da suka yi amfani da filin jirgin Esenboga a cikin watanni 11 sun kai miliyan 12 da dubu 719 da 565, yayin da zirga-zirgar jiragen sama ta kai dubu 92 da 134 kuma zirga-zirgar ababen hawa dauke da kayayyaki ta kai tan dubu 111 da 353.Labarai masu alaka