Ana fitar da kifi zuwa kasashen waje daga yankin Elazig na Turkiyya

Ana fitar da kifayen da ake kiwatawa a tafkunan Keban da Karakaya dake gundumar Kedan din lardin Elazig na Turkiyya.

Ana fitar da kifi zuwa kasashen waje daga yankin Elazig na Turkiyya

Ana fitar da kifayen da ake kiwatawa a tafkunan Keban da Karakaya dake gundumar Kedan din lardin Elazig na Turkiyya.

A watan Nuwamban 2019 a gundumar Keban an fitar da kifi nau'in Alabalik mai yawan tan dubu 18 da kuma tan dubu daya na nau'in somon.

Kusan tan dubu 10 na kifi nau'in Alabakil da ake kiwatawa a wajen an tura shi zuwa kasashen Jamus, Holan, Beljiyom da Rasha, somon kuma ya tafi zuwa kasashen gabas masu nisa da suka hada da Japan.

Turkiyya na kiwata kifaye nau'uka daban-daban tare da fitar da su zuwa kasashen waje da suke da bukata.Labarai masu alaka