An samu kari a adadin makamai da ake saida wa a duniya

An samu karin kaso 4.6 cikin adadin makamai da ake kera wa a duniya baki daya idan aka kwatanta adadin da na shekarar da ta gabata inda a lokaci guda Turkiyya ta shiga cikin jerin "Manyan kanfanoni guda 100 masu kera makamai a duniya."

Kungiyar Kididdiga Ta Zaman Lafiya wato SIPRI wanda babbar cibiyarta ke birnin Sitokuhom ta bayyana cewa manyan kanfanonin makamai guda 100 na duniya sun saida makamai masu darajar Dala biliyan 420 a shekarar 2018.

Kanfanonin Amurka ne su ke dauke da kaso 35 na makaman da aka saida inda darajar makaman ta kai Dala biliyan 148. 

Daga nan sai Rasha ta biyo bayanta da kaso 8.6 inda kasashen Turai ne ke biyo bayan Rasha da kaso 7.48.

A gefe guda kanfanonin Turkiyya guda 2 sun shiga cikin manyan kanfanonin guda 100 inda suka samu karin kaso 22 na adadin makaman da suka saida a wannan shekarar. Labarai masu alaka