'Yan kasar waje miliyan 12 ne suka ziyarci Istanbul

Gwamnan birnin Istanbul Ali Yerlikaya ya bayyana cewa 'yan kasar waje miliyan 12 da dubu 690 da 376 ne suka ziyarci birnin Istanbul daga farkon shekara zuwa karshen watan Oktoba.

Mista Yerlikaya ya yi bayanin ne ta shafinsa na twitter inda ya ce an samu karin kaso 11.91 idan aka kwatanta adadin da na shekarar 2018 inda kuma ya mika godiyarsa ga mutanen birnin domin karbar bakin da suka yi cikin nishadi.

Bayanin ya nuna cewa 'Yan Jamus ne suka fi kowa ziyartar birnin inda 'Yan Faransa ke biyo bayansu sai kuma 'Yan Kasar Ayilan da 'Yan Rasha suka biyo bayansu. 

 Labarai masu alaka