An yi garkuwa da ma'aikatan jirgin ruwa 19 da suka hada da Baturke 1 a gabar tekun Najeriya

An kai hari kan wani jirgin ruwan dakon man fetur a gabar tekun Najeriya inda aka yi garkuwa da mutane 19 da suka hada da dan kasar Turkiyya 1.

'Yan fashin tekun sun yi garkuwa da mutanen dake ckin jirgin ruwan dakon mai mai lambar Hong Kong inda suka yi awon gaba da 'yan kasar Indiya 18 da dan kasar Turkiyya 1.

Ba a bayar da bayan sunan Baturken da aka yi garkuwar da shi ba.

A ranar 3 ga watan Disamba ne aka kai hari kan irgin ruwar a gabar tekun tsaunin Bonny wadda kuma mallakar kamfanin dakon mai na Navios mallakin 'yan kasar Girka ne. Ana ci gaba da aiyukan ganin an kubutar da mutanen da aka yi garkuwar da su.

Masu garkuwa da mutane a gabar tekun Gini na yawan garkuwa da ma'aikata tare da neman fansa. A watan Yulin bana sun yi garkuwa da Turkawa 18 a lokacinda suka kai hari kan wani jirgin ruwan dakon mai.Labarai masu alaka