Lagarde: Kasashen Turai na iya afkawa matsalar tattalin arziki

Shugabar Babban Bankin Turai Christine Lagarde ta bayyana cewar bukatar kudi da tasarrufinsu ta ragu sosai a kasashen dake amfani da kudin Yuro.

Shugabar ta yi bayani ga kwamitin kudi da tattalin arziki na Majalisar Tarayyar Turai inda ta ce habakar kasashen ta ragu kuma na yin kasa sosai.

Lagarde ta tunatar da cewar tafiyar hawainiya da habakar tattalina rzikin ke yi ta shafi sha'anin kudi.

Ta ce "Ana ganin al'amuran kudia duniya na ci gaba da durkushewa. Wannan al'amari ya shafi sha'anin kudi da tasarrafinsu a kasashen dake amfani da kudin Yuro. Hakan na shafar zuba jari."

 Labarai masu alaka