Yawan 'yan kasar waje na cigaba da karu wa a Antalya

An samu karin kaso 17 cikin dari na 'yan kasar wajen dake ziyartar birnin Antalya ta hanyar jirgin sama inda adadin mutanen ya haura miliyan 15.

Yawan 'yan kasar waje na cigaba da karu wa a Antalya

An samu karin kaso 17 cikin dari na 'yan kasar wajen dake ziyartar birnin Antalya ta hanyar jirgin sama inda adadin mutanen ya haura miliyan 15. 

Kididdigar da aka yi tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba ta nuna cewa mutane sama da miliyan 15 da dubu 37 da 331 daga kasashe 193 ne suka ziyarci birnin inda adadin shekarar da ta gaba ya kasance miliyan 13 da dubu 642.

A gefe guda 'yar kasar Turkiyya guda dubu 593 da 80 ne suka ziyarci birnin.

'Yan Rasha ne a sahun gaba inda 'yan kasar Holan, Romeniya, Kazakistan, Cek da Suwidin suka kasance cikin kasashe 10 na farko. Labarai masu alaka