Asusun ajiyar rarar kudade na Turkiyya ya kusa dala 105

Babban Bankin Turkiyya ya sanar da cewar asusun ajiyar rarar kudadensu ya kai kusan dala biliyan 105.

Asusun ajiyar rarar kudade na Turkiyya ya kusa dala 105

Babban Bankin Turkiyya ya sanar da cewar asusun ajiyar rarar kudadensu ya kai kusan dala biliyan 105.

Babban Bankin ya fitar da alkaluman kudaden ajiya na rara na kasa da kasa na watan Oktoba.

Alkaluman da Bankin ya fitar sun nuna cewar kudaden rara na Turkiya a watan Oktoba sun karu da kaso 3,6 idan aka kwatanta da watan Satumba wanda a yanzu suka kama dala biliyan 104,6.

A wannan lokacin dai kudaden canjin kudin kasashen waje ya karu da kaso 3,8 wanda ya kama dala biliyan 76,5.

Adadin zinariya da ake da ita kuma ta kai ta karu da kaso 2,7 wanda ya kama dala biliyan 27..Labarai masu alaka