Trump ya soki manufofin kasuwancin Tarayyar Turai

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tsarin kasuwanci na Tarayyar Turai (EU) ya fi muni ta hanyoyi da yawa fiye da na China.

Trump ya soki manufofin kasuwancin Tarayyar Turai

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tsarin kasuwanci na Tarayyar Turai (EU) ya fi muni ta hanyoyi da yawa fiye da na China.

A cikin jawabin da Donald Trump ya gabatar a kungiyar kula da tattalin arzikin New York, ya soki Tarayyar Turai (EU) da China.

Trump ya bayyana cewa tsarin dokokin kasuwanci na Tarayyar Turai (EU) ba adalci bane ga masu kera kayayyaki na Amurka. Ya kuma ce 'Hanyoyin ciniki na Tarayyar Turai (EU) sun fi muni ta hanyoyi da yawa a kan na China.'

Trump kan tattaunawar kasuwanci tsakanin China da Amurka ya ce," China suna son a yi yarjejeniyar da gagawa amma mu ne za mu yanke shawara ko za muyi ko baza mu yi ba. Ba da jimawa ba amma muna gab da yin wata muhimmiyar yarjejeniya da kasar China, .'' Labarai masu alaka