Wasu kasashen Afirka za su kwashe kudadensu daga Babban Bankin Faransa

Shugaban Kasar Benin Patrice Talon ya bayyana cewar kasashen Yammacin Afirka sun cimma matsaya don kwashe kudadensu dake Babban Bankin Faransa.

Talon ya tattauna da kafafan yada labarai na Faransa inda ya bayyana cewar sakamakon yadda kasashen yammacin Afirka za su daina amfani da CFA su koma amfani da "eco" za su kwashe sauran kudadensu dake Babban Bankin Faransa.

Talon bai bayar da a wanne lokaci za a kwashe kudaden ba kuma idan aka kwashe za a tura su zuwa ga manyan bankunan kasashen da abun ya shafa.

Akwai kasashen Afirka rainon Faransa 14 da tun shekarar 1945 suka ajje kudadensu na CFA Frang Babban Bankin Faransa inda suka bar su a matsayin Euro domin kar darajarsu ta karye.

Tag: Eco , Afirka , CFA , Faransa

Labarai masu alaka