Satar man fetur tana shirin durkusar da Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 41.9 cikin shekaru 10 sakamakon satar man fetur daga ake yi daga rijiyoyin gwamnati.

Satar man fetur tana shirin durkusar da Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 41.9 cikin shekaru 10 sakamakon satar man fetur daga ake yi daga rijiyoyin gwamnati. 

An samo rahoton ne daga hannun Hukumar NEITI wanda ta shelanta cewa dole gwamnati ta magance matsalar cikin gaggawa inda har ana son tattalin arzikin kasar ya wanzu. 

Kididdigar ta nuna cewa ana satar man fetur din ne ta rijiyoyi da kuma bututun man fetur inda hakan ya sa ake anfani da kaso 1 cikin 5 na rijiyoyin man fetur din domin guje wa kaidin barayi. 

Najeriya na dauke da kaso 1 cikin 3 na man fetur din duniya inda take iya fitar da man fetur mai yawan ganga biliyan 37 a shekara. Labarai masu alaka