Kotu ta ci tarar Donald Trump

Wata kotu a birnin New York na Amurka, ta yankewa shugaban kasar Donald Trump hukuncin dala miliyan 2 saboda amfani da gidauniyar Trump Foundation don cin manufofin siyasa da kasuwanci.

Alkali Saliann Scarpulla ya umarci Trump ya biya dala miliyan biyu don cin amfani da gidauniyar Trump Foundation ta mummunar hanya don bukatun siyasa da kasuwanci.

Scarpulla ya yanke shawarar rufe Gidauniyar Trump tare da mayar da dala miliyan 1.7 zuwa wani gidauniyoyin.

A shekaran da ta gabata ofishin babban mai gabatar da kara na New York ya shigar da karar dala miliyan 2.8 da aka gabatar wa shugaban Amurka Trump da danginsa kan gidauniyar ta ayyukan jin kai. 

Tag: Tara , Kotu , Trump

Labarai masu alaka