Pekcan ta ce Brexit ba zai canja alakar Turkiyya da Ingila ba

Ministar Harkokin Kasuwancin Turkiyya Ruhsar Pekcan ta bayyana cewa “alakar Turkiyya da Ingila baza ta canja ba bayan Brexit, bilakis kara habaka za ta yi”.

Misis Pekcan ta yi jawabi a babban taron kasuwanci da aka tsakanin dakarun Turkiyya da na Ingila inda ta ce tana farincikin shaida taron da yau shekara 10 kenan ana yin irinsa.

Misis Pekcan ta bayyana cewa a shirye suke su yi ayyuka a fannin fasaha inda ta shaidawa takwaranta ta Ingila Elizabeth Truss cewa Turkiyya za ta kafa cibiyoyi guda 10 domin gudanar da ayyukan fasaha.

Ta cigaba da cewa, “ya kamata mu yi hadin gwiwa a fanni kimiyya da fasaha. Inada tabbas din cewa Turkiyya na da kere-keren fasaha da Ingila zata anfanu da shi. Sannan mun san irin jajircewan da kanfanonin Ingila ke yi a fanni fasaha. Wannan hadin gwiwa ne da zai taimakawa kasashen mu biyu.”Labarai masu alaka