Tauraron dan adam na "Yaogan-33" da China ta harba sama ya fado

Tauraron dan adam samfurin "Yaogan-33" da China ta harba sama da nufin daukar bayanai daga nesa ya fado.

Tauraron dan adam na "Yaogan-33" da China ta harba sama ya fado

Tauraron dan adam samfurin "Yaogan-33" da China ta harba sama da nufin daukar bayanai daga nesa ya fado.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayyana cewa, an tura Yaogan-33 zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba taurarin dan adam zuwa sama ta Taiyuen inda aka yi amfani da kumbon Long March-4C.

Bayan an harba tauraron a mataki na farko da na biyu yana aiki yadda ya kamata amma a mataki na 3 sai ya samu matsala.

Bayan wani dan lokaci tauraron ya fado kasa tare da kumbon da aka jefa shi.

Ba a bayar da bayanan a ina ne buraguzan tauraron dan adam din suka fado ba amma an fara gudanar da bincike.

A watan Afrilun shekarar 2018 tauraron Tiangong-1 da China ta harba ya fado a kudancin yankin Pacific.

China na son nan da shekarar 2045 ta zama jagorar duniya wajen bincike a sararin samaniya inda take harba taurarin dan adam masu daukar bayanai daga nesa.Labarai masu alaka