Mutane 8 daga cikin masu yajin cin abinci sun mutu a Mali

Ma'aikatan lankwasa karafa 8 sun rasa rayukansu watanni 4 bayan fara yajin cin abinci sakamakon rashin biyan su albashi a Mali.

Mutane 8 daga cikin masu yajin cin abinci sun mutu a Mali

Ma'aikatan lankwasa karafa 8 sun rasa rayukansu watanni  4 bayan fara yajin cin abinci sakamakon rashin biyan su albashi a Mali.

Labaran da shafin News.abamako ya fitar na cewa, tsawon watanni 11 ma'aikatan ba su karbi albashi ba wanda hakan ya sanya su fara yajin cin abinci tun daga ranar 18 ga watan Disamban 2018 zuwa yau, kuma a yanzu takwas daga cikin su sun mutu.

Ma'aikatan na aiki a kamfanin sarrafa bakin karfe na gwamnatin Mali.

An kai ma'aikatan da dama zuwa asibiti sakamakon yadda yanayin lafiyarsu ya munana.

A gefe guda kuma malaman makaranta a Mali sun yi alkawarin fara yajin aiki har nan da 17 ga watan Mayu.

Malaman na neman a saukaka musu hanyoyin cin bashin sayen gidaje da amfana da romon aiyukan gwamnati a kasar.Labarai masu alaka