An bayar da umarnin kama tsohon Ministan Iraki bisa zargin cin hanci da rashawa

A Iraki an bayar da umarnin kama wa tare da tuhumar mutane 32 da suka hada da tsohon Minista wadanda ake zargi da aiyukan cin hanci da Rashawa.

Shugaban Hukumar Kula da Ingancin Aiyukan Gwamnati Izzet Taufiq ya fada wa manema labarai a birnin Baghdad cewa, a shekarar 2018 sun tantance takardun aiyukan cin hanci dubu 12,398 tare da samun sakamakon kaso 70 cikin 100 nasu.

Taufiq ya kuma ce, a takardun da suka tantance sun gano akwai tsaffin Ministoci da Masu ci a yanzu su 15 da hannu a aiyukan cin hanci da rashawa.

Baya ga su din akwai wasu manyan jami'an gwamnati su 17 da su ma aka bayar da umarnin kama su tare da gurfanarwa a gaban kotu.

Shugaban ya kara da cewa, a shekarar 2018 akwai aiyuka dubu 2,736 da aka dakatar kuma an shigar da kara game da 644 daga cikinsu. Jami'İn na Iraki bai bayar da bayanai kan wadannan aiyukan ba.Labarai masu alaka