"OPEC na buƙatar gyara"

Ministan harkokin man fetur ɗin ƙasar lran Bijen Namdar Zengene ya bayyana cewar akwai bukatar a duba yunƙurin ficewar ƙasar Katar daga ƙungiyar ƙasashe masu albarkatun man fetur wato OPEC.

"OPEC na buƙatar gyara"

Ministan harkokin man fetur ɗin ƙasar lran Bijen Namdar Zengene ya bayyana cewar akwai bukatar a duba yunƙurin ficewar ƙasar Katar daga ƙungiyar ƙasashe masu albarkatun man fetur wato OPEC.

Kanfanin dillancin labaran majalisar ƙasar lran  lCANA ta sanar da cewa minista Zengene ya yi wata sanarwa gabanin taron ƙolin ƙasashen ƙungiya masu albarkatun manfetur OPEC da za'a gudanar a Vienna babban birnin kasar Austria.

Zengene da yake bayyana cewar Katar ta yanke hukuncin ficewa daga kungiyar ne sabili da wasu manyan matsaloli da take da shi da wasu manyan ƙasashe daga cikin kungiyar, ya ƙara da cewa:

"Ya kamata a duba lamurkan da suka sanya ƙasar Katar yunkurin ficewa daga ƙungiyar ƙasashe masu albarkatun manfetur"

Wakilin kungiyar ƙasashen masu albarkatun manfetur a ƙasar lran Hussaini Kazimpur Erdebili ya bayyana cewar matakan da ƙasashen Saudiyya da Rasha suka dauka dangane da fitar da manfetur na ƙashin kansu ne ya sanya Katar yanke hukuncin fita daga kungiyar.

Ana dai tunanin a taron ƙolin kungiyar ƙasashen masu albarkatun manfetur da za'a gudanar za'a dauki matakan rage fitar da yawan man fetur a duniya.

Ministan harkokin kimiyya da fasaha na kasar Katar Saad Sherida el Kabi ne ya fitar da sanarwar cewa Katar zata fita daga cikin ƙasashen OPEC.

Katar dai ta kasance mambar ƙasashen masu albarkatun manfetur tun daga shekarar 1960.

 

 Labarai masu alaka