Asibitin kula da lafiyar tankokin yaki dake garin Kayseri na Turkiyya

Mun sake kasance watare da sharhin Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kamfanunnukan Samar da Kayan Tsaro dake Turkiyya Tarkan Zengin.

Asibitin kula da lafiyar tankokin yaki dake garin Kayseri na Turkiyya

Yadda kamfanunnukan samar da kayan yaki suke a kasarmu na nuna yadda aka samar da aiyuka masu muhimmanci. A bangaren aiyukan soji da yaki da ta’addanci a Turkiyya na bayyana irin muhimmanci da wadannan aiyuka suke da shi. A shekarar 1951 aka fara aikin gyara motocin yaki a Masana’anta ta 2 dake garin Kayseri. Wannan kamfani, an bude a shekarar ta 1952 da sunan mai gyara kayan rundunar soji ta 1020. A shekarar 1987 an canja sunan Masana’antar zuwa ta runduna ta 1009. A shekarar 2003 kuma ta zama babbar Masana’antar gyara kayan yakin rundunar sojin Turkiyya. Saia 2016 da ta koma Hukuma ta 2 Mai Kula da Masana’antun gyara kayan yaki na Turkiyya. Akwai kusan mutane 800 dake aiki a wannan masana’anta. Akwai leburori 480 sauran kuma sun hada da kananan sojoji da fararen hula dake aiyukan gudanarwa. Suna ci gaba da aiyyukansu cikin nasara.

Hukuma ta 2 Mai Kula da Masana’antun gyara kayan yaki na Turkiyya,  ta kasance tana dubawa tare da gyara motocin dakarun Turkiyya na yaki, sabunta su da yi musu kwaskwarima. Tana sake sassansu da samar da wasu sababbi. Irın wadannan motocin yaki sun hada da tankoki, Igwa da masu sulke samfurin (ZPT). Haka nan kuma akwai motocin yaki samfurin (ZMA), motocin harba bama-bamai masu sulke (ZMA) da sauransu. Hukuma ce dake bayar da dukkan wani taimako ga rundunar sojin Turkiyya. Ga wasu jerin aiyyka da ake yi a Hukuma ta 2 Mai Kula da Masana’antun gyara kayan yaki na Turkiyya dake Kayseri:

  1. Bangarorin motocin yaki,
  2. Sauya mai tare da saka shi a cikin wadannan motoci,
  3. Maganadisun lantarki na motocin yaki,
  4. Ba wa ‘yan kasashe kawayen Turkiyya horo a wajen,
  5. Bayan da shawarwari ga dakarun tsaron Turkiyya.

AN SABUNTA IGWA SAMFURIN M-60

Tun bayan da aka fara samar da irin wadannan motoci masu kacha, ana ci gaba da sabunta su, mayar da su na zamani. Saboda irin kwarewar da ake da ita an an samu damar zamantarwa tare da sabunta tankokin yaki na Igwa samfurin M48AT1-T2 har sama da guda dubu biyu. An samu nasarar samar da tankar TAMAY. Makamin yaki na (ISA), tanlar igwa mai iya hawa tsaunuka. Haka zalika, a wajejan shekarar 2000 an sabunta ma’aciyar mai ta M113 ZPT wadda aikinta ya kara karfi sosai tare da mayar da ita samfurin M113 A2T2. Wasu daga cikin wadannan kayan yaki na motoci sun samu nasarar zama manyan motocin yaki, na zamani da suke biyan bukatun Rundunar Sojin Turkiyya.

A shekarun da suka kare, an kammala samar da tankokin yaki samfurin M60T da MLC 70 mai hawa gadoji. Tankar M60T da aka sabunta, ta samu a karon farko ta ingantu da fasahar sulke mai sarrafa kanta wato (Explosive Reactive Armour/ERA). Bayan an sabunta su tare da saka musu tayoyin kacha sai suka koma na zamani sosai inda akasauya sunansu zuwa M-60 T wato harafin t din na nufin Turkiyya. Wannan motoci su 170 na hidima ga dakarun Turkiyya. A wani batun kuma, an sake sabunta wadannan tankokin yaki na M60-T. Haka zalika bayan an sabunta wadannan motocin yaki, an samar da waje na gwajin amfani da su. Har yanzu a Kayseri a wanna Masana’anta ta 2 ana ci gaba da aikin samar da tankokin yaki na zamani samfurin (ADOP-2000) da 2A4 masu iya harba manyan bama-bamai.

 

WAJEN DAKE BAYAR DA TAIMAKON AIYUKAN KASA

A Hukuma ta 2 Mai Kula da Masana’antun gyara kayan yaki na Turkiyya, ta bayar da taimako wajen samar da injinan yaki da da tankoki a hare-haren da aka kai na tsaron yankin Firat, da hare-haren Reshen Zaitun da aka kaddamar da su a yankin Afrin na Siriya a shekarun 2016 da 2017. Haka zalika, Hukumar ta gyara motoci masu kacha da suka lalace. Hakan ya sanya yawan kayan da ake gyrawa ya ribanya har sau biyu sannan taimakon da ake bayarwa ya inganta sosai. Kuma tun farkon fara kai hare-haren har zuwa karshensu, Hukumar ta aike da ma’aikatanta dake wkashe dukkan motocin da suka lalace tare da gyara su a ciki da wajen Turkiyya. Wadannan ma’aikata da suka hada da leburori da sojoji sun je yankunan Afrin da aka kaddamar da tsaron Firat da reshen Zaitun.

WAJEN AIKI DAKE DA YA SAMU KAMBI DA YAWA

Hukuma ta 2 Mai Kula da Masana’antun gyara kayan yaki na Turkiyya DAKE Kayseri, sakamakon kyakkyawan aiyuka da take yi ta samu kyaututtuka da dama da suka hada AQAP-2110 wadda Rundunar Tsaro ta NATO take bayarwa idan ta amince da kyawun aiyuka wani kamfanin samar da makamai. Haka zalika an samu kambi saboda kula da muhalli wato kambin TS EN ISO 14001. Haka zalika an ba wa Hukumar kambin OHSAS 18001 dake tabbatar da tana kula da lafiya da rayukan ma’aikatanta da yanayin aikinsu. Hukuma ta 2 Mai Kula da Masana’antun gyara kayan yaki na Turkiyya na bayar da muhimmanci sosai wajen ganin aiyukanta sun inganta matuka. A ranar 4 ga watan Maris din 2014 Hukumar ta samu kambi daga Hukumar tabbatar da inganci kayayyaki ta Turkiyya. A ranar 18 ga watan Oktoban 2017 kuma ta zama Hukuma ta farko da ta samu kambin Inganci Kayayyakin Kasa. Ma’aikatar tsaro ta Turkiyya ta zabi Hukuma ta 2 Mai Kula da Masana’antun gyara kayan yaki na Turkiyya a matsayin kamfanin matuka jiragen sama inda ta ba ta kambi mai taurari 3.  Labarai masu alaka