Sakamakon taron kolin kasashen G20 a Argentina

A tsakanin ranakun 30 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba an ka gudanar da taron ƙolin ƙasashen G20 a Buenos Aires babban birnin kasar Argentina.

Sakamakon taron kolin kasashen G20 a Argentina

A tsakanin ranakun 30 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba an ka gudanar da taron ƙolin ƙasashen G20 a Buenos Aires babban birnin kasar Argentina. Wannan kungiyar mai ainihin mambobi 20 tana tattara ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki da masu tasowa domin tattaunawa akan harkokin tattalin arziki na yau da kullum. Daga cikin mambobin wannan ƙungiya 20 sun haɗa da Kanada, Faransa, Ingila, Jamus, Koriya ta Kudu, ltaliya, Japan, Ostraliya, Tarayyar Turai, lndonisiya, Turkiyya, Argentina, lndiya, Brazil, Saudiyya, Mexico, China, Rasha da Afirka ta Kudu.

Baya ga wadannan ƙasashen akwai wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa dake halartar tarurrukanta. Daga cikinsu akwai Hukumar Kasuwanci ta Duniya, Asusun Bayar da tallafi ta lMF da Hukumar Kwadago ta ƙasa da ƙasa da kuma babban Bankin Duniya.

A wannan sabuwar maudu'in mun sake kasancewa tare da ferfesa Erdal Tanas KARAGÖL malaminmu a sashen nazarin siyasa da tattalin a jami'ar Yıldırım Beyazıt.

Shin ko menene muhimmancin aiyukan wannan kungiyar? Mambobin wannan kungiyar ke da mallakar kuɗaɗe da dukiyar duniya har na kaso 85 cikin ɗari, haka kuma kaso 75 cikin ɗari kasuwancin duniya na hannunta. Kashi biyu cikin ukun mutanen duniya na zama ne a cikin wadannan ƙasashe. Sabili da haka dukkan matakan da G20 zata dauka a sassan kasuwanci, ilimi, kimiyya, fasaha da siyasa zai shafi kowa.

Wannan kungiyar da aka kafa a shekarar 2009, ta samu asali kasancewar rikicin tattalin arzikin kasashen Asiya. Harr izuwa shekarar 2008 shugabannin manyan bankunan ƙasashen ne kawai ke taruwa a taron ta, amma daga 2008 kawo yanzu har da shugabannin siyasar ƙasashen na taruwa su gana da juna.

Ƙafa kungiyar G20 ba wai domin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki bane kawai, har ma da kasashe masu tasowa. Saboda haka G20 ta kasance lasafikan ƙasashe masu tasowa kamar Turkiyya a sassan tattalin arziki a duniya.

Kamar ko wacce shekara; wannan shekarar ma an fitar da sakamakon taron ƙolin. Sakamakon taron ya nuna cewa Hukumar Kasuwanci ta Duniya bata yin aikinta kamar yadda ya kamata. Sabili da hukumar ce keda alhakin samar da daidaito a kasuwanci duniya tare da kare dukkanin matsaloli da rikice-rikice da ka iya tasowa. Duk da haka, a fadin duniya an samu rikicin kasuwanci tsakanin ƙasashe. A gaskiyar lamarin sakamakon taron ya nuna rashin ingancin matakin da Amurka ta dauka akan lamurkan kasuwanci tsakanin ƙasashe.

Haka kuma sakamakon taron ya kunshi lamurkan haddin kai dangane da kasuwanci, ci gaban ƙasashe, samar da wadataccen abinci, daidaito tsakanin jinsi da makamantansu. Sabili da haka an aminta akan cewa hanyar da za'a tabbatar da daidaito da adalci ita ce ta lumana da fahimtar juna.

  An kuma tattauna akan bunƙasa jin dadin bil adama ta hanyar inganta lamurkan aiki ta hanyar bayar da ilimi, gyara guraren aiki da ƙarawa ma'aikata ƙarfin gwiwa a ƙasashe. Bayan haka an kuma duba yadda za'a inganta harkokin fasahar yara mata ta hanyar da zasu fa'idantu suku ma bada nasu gudunmawa. Bugu da ƙari an kuma duba yadda za'a inganta koyar da yara mata da manyan mata iya amfani na na'urorin kimiyya da fasaha da kuma lissafi.

Wani bangaren da aka tattauna akai kuma, ita ce yarjejeniya ɗumaman yanayi ta Paris, inda aka muhimmanci mutunta yarjejeniyar baya ga Nahiyar Turai, lamarin da aka yi a’manna da zai warware matsalolin dumamar yanayi a yankin baki daya. Lamari na karshe da sakamakon taron ƙolin G20 ya kunsa shi ne lamarin yan gudun hijira, an tattauna akan yadda za'a inganta rayuwar yan gudun hijira, kasancewar matsala ce da ta shafi dukkan ƙasashe da kuma ya kamata su dauki kwararan matakai akai.

Bugu da ƙari, an amince da za'a gudanar da taron ƙolin G20 na shekarar 2019 a ƙasar Japan, a shekarar 2020 kuma a Saudiyya.

Wannan sharhin ferfesa Erdal Tanas KARAGÖL ne malami a sashen ilimin siyasa da tattalin arziki a jami'ar Yıldırım Beyazıt dake nan Ankara babban birnin ƙasar Turkiyya.

 Labarai masu alaka