Tattalin arzikin Kazagystan ya samu tagomashi

Ministan tattalin arzikin Kazagystan Timur Suleyman ya bayyana cewar tattalin arzikin ƙasarsa ya bunƙasa a cikin watanni takwas na farkon shekarar bana da kaso 3.8 cikin ɗari.

Suleyman ya jaddada habbakar tattalin arzikin ƙasar daga watan Janairu zuwa Agusta a taeta ƙolin ministocin ƙasar, inda ya kara da cewa: 

"Duk da irin kalubalen da tattalin arziki ke fuskanta a duniya, tattalin arzikin Kazagystan ya samu habbaka a cikin watanni takwas na farkon shekara da kaso 3.8 cikin ɗari."

Suleyman ya bayyana cewar anyi hasashen tattalin arzikin kasar zai karu da kaso 4 cikin ɗari.

Suleyman ya karada cewa daga daya ga watan Satumba yawan kuɗaɗen da kasar ke ajiyewa a asusun ta na waje yakai dala biliyan 87.3, inda yawan zinarinta ya karu da kaso 0.1 cikin ɗari a yayinda yakai na dala biliyan 30.8.

 Labarai masu alaka