An sace Lu'u-Lu'in Gimbiyar Saudiyya a wani otel a Faransa

A Paris Babban Birnin Faransa an sace Mujauharin Gimbiyar Masarautar Saudiyya da ya kai darajar Yuro dubu 800 a wani otel da ta ke zama.

An sace Lu'u-Lu'in Gimbiyar Saudiyya a wani otel a Faransa

A Paris Babban Birnin Faransa an sace Mujauharin Gimbiyar Masarautar Saudiyya da ya kai darajar Yuro dubu 800 a wani otel da ta ke zama. 

Labaran da jaridar France Blue ta fitar na cewa, an sace Lu'u-Lu'in a ranar Juma'ar da ta gabata.

A labaran an kuma ce, Gimbiyar ta sauka a wani babban otel da ke dandalin Vendome na Paris kuma bayan ta gano an sace kayan nata sai ta sanar da jami'an tsaro.

Labaran sun ce, ba a boye Lu'u-Lu'in a wani waje na musamman ba, kuma ba a ga alamun an balla kofar dakinta ba.

A wani shagon sayar da Lu'u-Lu'i da ke otel din a shekarar da ta gabata an sace wanda ya kai darajar Yuro miliyan 4.

Wasu 'yan fashi su 5 da suka rufe fuskokinsu ne suka saje Lu'u-Lu'in amma cikin kankanin lokaci aka kama 3 daga cikinsu.

 Labarai masu alaka