Mutane 8 sun mutu a wata gobara da ta kama a Afirka ta Kudu

Mutane 8 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wata gobara da ta kama a kamfanin Denel Munition da ke garin Cape Town na Afirka ta Kudu.

Mutane 8 sun mutu a wata gobara da ta kama a Afirka ta Kudu

Mutane 8 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wata gobara da ta kama a kamfanin Denel Munition da ke garin Cape Town na Afirka ta Kudu.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Cape Town Theo Layne ya bayyana cewa, har yanzu ba a gano musabbabin fashewar wasu abubuwa a kamfanin ba wanda suka janyo kamawar wutar.

Kamfanin shi ne mafi girma a Afirka ta Kudu wajen samar da kayan sojoji.

An bayyana cewar wasu karin mutane 4 sun jikkata a lamarin.

Sauran kamfanunnukan samar da makamaina Afirka ta Kudu sun aike da sakon jaje ga masu kamfanin da gobarar ta kama.

Kaso 51 na kamfanin mallakin Turawan Jamus ne.Labarai masu alaka