China ta aike da sakon ba sani ba sabo ga Amurka

A China ta aike da sakon ba sani ba sabo da ramuwar gayya ga Amurka inda ta ce za ta kara wa Kasar haraji ninki ba ninki kan kayan da ta ke shigarwa Kasarta.

Ma'aikatar Kasuwanci ta China ta fitar da sanarwa bayan fara aiki da sabon tsarin haraji da Amurka ta sanya inda ta ce, tun a farkon yakin kasuwanci China ta ce ba za ta harba nata harsashin ba amma kuma za ta kare martabar al'umarta.

Sanarwar ba ta bayar da sabbin matakan da China za ta dauka ga Amurkan ba.

A bayan gwamnatin China ta ce, za ta sanya harajin dala biliyan 50 ga kayan fasaha da Amurka ke shigarwa kasarta a matsayin ramuwar gayya ga dala biliyan 34 da ita ma Amurkan ta ce ta sanya wa China kan dukkan kayan fasaha da ta ke shigarwa Amurkan. 

 Labarai masu alaka