Za'a gudanar da gagarumar zanga-zangar ƙalubalantar manufofin gwamnatin Faransa

Kungiyar kwadagon kasar Faransa da haddi gwiwar kungiyar ma'aikata sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga a ranar 28 ga watan Yuni domin kare hakkokin ma'aikata, marasa aikin yi, waɗanda suka yi ritaya da ɗaliban kasar.

Da yawan kungiyoyi sun aminta akan zanga-zangar da za'a gudanar, inda kuma suka bayyana cewar zasu zauna a watan Agusta domin daukar matakan da suka dace akan lamarin.

Domin ƙalubalantar sabon tsarin tsunke ajihu da sauya lumurkan aiki miliyoyin mutane sun yi amanna da yajin aiki.

Wannan ne dai karon farko da kungiyoyin ma'aikatar kasar suka yi kira bai ɗaya da a gudanar da zanga-zanga hadi da yajin aiki domin ƙalubalantar sabbin tsarukan aikin gwamnati na shekarar 2016.

Ana dai hasashen za'a ci gaba da yajin aiki ƙalubalantar tsarin tsunke ajihu da gwamnatin kasar ta fitar.

 Labarai masu alaka