Kungiyar OPEC za ta gudanar da taro a birnin Istanbul

Kungiyar Kasashe Masu fitar da albarkatun man fetur za ta gudanar da babban taro a ranar Alrabar nan a birnin ıstanbul inda za ta tattauna batun rage yawan man fetur din da suke fitarwa.

Sakatare Janar na Kungiyar Muhammad Barkindo ya amsa tambayoyin manema labarai bayan jawabin da ya yi a wajen taron cigaban makamashi karo na 23 da ake a birnin Istanbul.

Shugaban na OPEC ya ce, lallai akwai bukatar a rage yawan man da ake fitarwa wanda da ma a watan da ya gabata ya bayyana haka a yayin wani taro a kasar Aljeriya.

Barkindo ya ce, wannan taro na Ustanbul ya bayar da dama sosai na kasashen su zauna su tattauna a tsakaninsu domin samun mafuta, inda ma za su iya tattaunawa da kasashen da ba sa fitar da man.

Barkindo zai kuma gabatar da taron manema labarai bayan kammala ganawar tasu a ranar Larabar nan.Labarai masu alaka