Erdogan: Idan aka amince da sharuddanmu za mu kula da filin jiragen sama na Kabul

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, idan aka amince tare da samar da sharuddan da za su gindaya, to za su amince tare da karbar aikin kula da filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul Babban Birnin Afganistan.

1677750

A jawabin da Shugaba Erdogan ya yi a Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus ya ce,

"An shiga wani sabon babi don samar da tsaro a filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul. Ana kallon masu fada a ji 3 a wannan waje. NATO, Amurka da Turkiyya. Amurka ta amince ta janye gaba daya. Da ma tsawon shekaru 20 kenan bangarenmu ke kula da filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul kuma a yanzu ma suna son ci gaba da kula da shi."

Shugaba Erdogan ya kuma bayyana cewa, suna da sharuddan da suka bayyanawa Amurka game da wannan batu.

Ya ce, "A yanzu muna kallon akwai yiwuwar Turkiyya ta kula da filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul. Amma a lokacin da hakan ke faruwa muna da sharuddan da muke so Amurka ta kalla. Na farko shi ne game da diplomasiyya Amurka za ta kasance tare da mu, na biyu kuma za ta ba mu dukkan kayan aikin da muke bukata. Duk wani abu na aiki za a mikawa Turkiyya shi. Sannan na ukun shi ne za a fuskanci matsalolin kudi don gudanar a aiyukan. A nan ma za a baiwa Turkiyya taimakon da ya kamata. Idan za a amince da wadannan sharudda to Turkiyya za ta iya amincewa da karbar aikin kula da filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul."

Ya ci gaba da cewa, 'Yan Taliban suna da damuwa game da batun, kuma akwai abubuwan da Taliban ta tattauna da Amurka wanda da Turkiyya ne ya kamata ta tattauna su.Labarai masu alaka