Majalisar Shugabanci ta Libiya ta gargadi Italiya

Majalisar Shugabanci ta Libiya ta gargadi Italiya kan ta daina shiga harkokinta na cikin gida.

1662996
Majalisar Shugabanci ta Libiya ta gargadi Italiya

Majalisar Shugabanci ta Libiya ta gargadi Italiya kan ta daina shiga harkokinta na cikin gida.

Majalisar ta yi wannan gargadi sakamakon yadda Italiya ke yunkurin shirya wani taro na sulhun kasa game da Libiya a kasarta ba tare da sanin gwamnatin Libiyan ba.

Shugaban Majalisar Muhammad Al-Manfi ya shaida cewa, game da wannan batu ya aike da sako ga Ministar Harkokin Wajen Libiya Najla Al-Mankush.

A sakon nasa, Al-Manfi ya shaida cewa, an samu labarin Ma'aikatar Harkokin Wajen Libiya za ta aike da wakilai daga yankin Fizan na kudancin kasar zuwa wani taro na sulhun kasa da Italiya ta shirya a kasarta.

Majalisar ta soki wannan mataki na Italiya kuma ta bukaci da ta soke gudanar da wancan taro.

Haka zalika sakon ya gargadi Italiya da ta daina tsoma hannu da katsalandan a cikin harkokin cikin gidan Libiya.Labarai masu alaka