Guterres: MDD za ta hada kai da Iran don cigaban jama'ar kasar

Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya fitar da sakon da mai gidansa Antonio Guterres ya fitar game da nasarar da Ibrahim Reisi ya yi a zaben Shugaban Kasar Iran da aka yi a ranar Juma'ar da ta gabata.

1662423

Ya ce, "Sakatare Janar Guterres ya bayyana cewa, suna jiran su hada kai da shugabannin Iran domin samar da ci gaba da kare manufofin jama'ar kasar da ma yankin baki daya."

A yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a helkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, Dujarric ya kara da cewa, za a bibiyi halin da ake ciki, kuma akwai tsawon makonni 6 kafin a mika mulkin Iran ga Reisi.

A ranar 18 ga Yuni aka gudanar da zaben Shugaban Kasa a Iran inda Ibrahim Reisi ya samu kaso 62 na kuri'un da aka jefa tare da zama Shugaban Kasar na 8.Labarai masu alaka