Isra'ila ta saki Shaikh Al-Khatibi

Kotun Isra'ila ta yanke hukuncin sakin Mataimakin Shugaban Gwagwarmayar 1948 ta Falasdinawa Shaikh Kamal Al-Khatibi.

1661693
Isra'ila ta saki Shaikh Al-Khatibi

Kotun Isra'ila ta yanke hukuncin sakin Mataimakin Shugaban Gwagwarmayar 1948 ta Falasdinawa Shaikh Kamal Al-Khatibi.

Kafar yada labarai ta KAN mallakar Isra'ila ta bayyana cewa, alkalin kotun yankin Nasira ya yi watsi da bukatar masu gabatar da kara na jinkirta lokacin sakin Al-Khatibi da awanni 48.

Tare da sakin Al-Khatibi an gindaya masa sharuddan ba zai zanta da manema labarai ba, ba zai yi Khuduba ko yin jawabi ga taron jama'a ba, ba zai koma unguwar da yake zama ta Kafr Kanna har nan da kwanaki 45 ba, ba zai yi wani rubutu a shafukan sada zumunta ba sannan ba zai zauna tare da mutane sama da 15 ba.

Ofishin Gabatar da Kara na Isra'ila ya samu Al-Khatibi da laifin zama mamban kungiyar Gwagwarmayar 1948 ta Falasdinawa wadda Isra'ila ta haramta da kuma saburar da jama'a su aikata laifi.

A ranar 14 ga Mayu ne aka kama Al-Khatibi a gidansa da ke unguwar Kafr Kanna.

Kwana guda bayan kama shi aka gurfanar da shi a gana kotu, kuma sakamakon wasu dalilai aka dinga kara kwanakin rike shi.

 Labarai masu alaka