Guguwar "Claudette" ka iya jefa mutum miliyan 7 cikin mawuyacin hali a Amurka

An yi wani sabon gargadi game da guguwar "Claudette" wanda zai iya shafar mutane miliyan 7 da ke zaune a gabar tekun kudancin Amurka

1661149
Guguwar "Claudette" ka iya jefa mutum miliyan 7 cikin mawuyacin hali a Amurka

An yi wani sabon gargadi game da guguwar "Claudette" wanda zai iya shafar mutane miliyan 7 da ke zaune a gabar tekun kudancin Amurka.

A cikin sabon sabuntawa na Cibiyar Guguwa ta Kasa (NHC), an bayyana cewa guguwar mai karfi da ake kira "Claudette" ana sa ran za ta isa yankin Amurka daga gabar Louisiana.

A shafin yanar gizon NHC, an yi rikodin cewa ruwan sama mai karfi da iska daga Tekun Mexico sun fara isa yankin Amurka daga safiya, suna barazana ga mutane miliyan 7 da ke zaune a yankin daga Louisina zuwa Florida.

Gwamnan Louisiana John Bel Edwards ya ce:

"Ofishin Gwamna na Tsaron Cikin Gida da Shirye-shiryen Cikin Gaggawa (GOHSEP) ya tattara kungiyar masu daukar matakan rikicin, kuma tare da abokan hadin gwiwarmu na gida, mun kasance a shirye don kowane irin yanayin da ake bukata."
 Labarai masu alaka