Shugaba Erdogan ya tattauna da Sarkin Saudiyya ta wayar tarho

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz.

1634167
Shugaba Erdogan ya tattauna da Sarkin Saudiyya ta wayar tarho

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz.

Sanarwar da Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya ya fitar ta ce, an tattauna kan alakar Turkiyya da Saudiyya.

Shugaba Erdogan ya kuma mika sakon taya murna ga Sarki Salman bisa daren Lailatul Qadri da za a riska a makon nan.

Haka zalika an tattauna kan batutuwan hadin kai da al'amuran da suka shafi bangarorin 2.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da Shugaba Erdogan da Sarki Salman suka gudanar a ranar 21 ga Nuwamban 2020, an tattauna kan alakar kasashen 2, sannan an yi nazari da duba ga shugabancin G20 da Saudiyya ke yi a lokacin.

Erdogan da Salman sun aminta kan bunkasa alakar kasashensu tare da tafiyar da dukkan wasu matsaloli da ake fuskanta ta hanyar tattaunawa.Labarai masu alaka