Cavusoglu ya tattauna da takwarorinsa na Libiya da Malta

Ministocin Harkokin Wajen Turkiyya, Libiya da Malta sun gudanar da taron 'yan uku a Ankara.

1620132
Cavusoglu ya tattauna da takwarorinsa na Libiya da Malta

Ministocin Harkokin Wajen Turkiyya, Libiya da Malta sun gudanar da taron 'yan uku a Ankara.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa, sun gana tare da Ministar Harkokin Wajen Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Libiya Nejla Al-Mangush da Ministan Harkokin Wajen Malta Evarist Bartolo.

A sakon da Cavusoglu ya fitar ya ce,

"A wannan gaba za mu ci gaba da bayar da goyon baya don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Libiya. Za a ci gaba da hada kai a tsakaninmu don yaki gudun hijira ba bisa ka'ida ba a tekun Bahar Rum tare da samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin."Labarai masu alaka