Turkawa zasu fara ziyarar Azabaijan ba tare da visa ba

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewa an kammala shirin da zai baiwa Turkawa da ‘yan kasar Azabaijan damar shiga kasashen juna ba tare da takardan visa ba

1614433
Turkawa zasu fara ziyarar Azabaijan ba tare da visa ba

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewa an kammala shirin da zai baiwa Turkawa da ‘yan kasar Azabaijan damar shiga kasashen juna ba tare da takardan visa ba.

Kamar yadda ya yada a twitter Cavusoglu ya bayyana cewa, An cire dukkanin shinge a ziyarar juna tsakanin Azabaijan da Turkiyya. A halin yanzu ‘yan kasashen biyu zasu iya ziyarar juna da katin shaidan zaman yan kasashensu kawai.

‘Yan kasar Turkiyya zasu fara iya ziyarar kasar Azabaijan ba tare da fasafort da visa ba, kawai abinda zasu nuna shi ne takardan shaidan zama ‘yan kasa.Labarai masu alaka