Oktay zai halarci bukin rantsar da sabon Shugaban Kasar Nijar

Mataimakin Shugaban Kasar Turkiyya Fuat Oktay zai halarci rantsar da sabon zababben Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum wanda za a yi a ranar Juma'a 2 ga Afrilu.

1613136
Oktay zai halarci bukin rantsar da sabon Shugaban Kasar Nijar

Mataimakin Shugaban Kasar Turkiyya Fuat Oktay zai halarci rantsar da sabon zababben Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum wanda za a yi a ranar Juma'ar nan 2 ga Afrilu.

Ana sa ran Oktay zai yi ganawa da Shugabannin Nijar bayan kammala taron rantsuwar a babban dakin taro na Mahatma Ghandi da ke Yamai Babban Birnin Nijar.

A zagaye na biyu na zaben da aka yi a ranar 21 ga Fabrairu, dan takarar jam'iyyar mai mulki ta PNDS-Tarayya Mohammed Bazoum ne ya yi nasara.

 Labarai masu alaka