Tangardan alaƙar Turkiyya da Amurka

Maso sauraronmu barkammu da wannan lokaci a cikin wani sabon shirinmu na sharhin al’amurran yau da kullum

1587369
Tangardan alaƙar Turkiyya da Amurka

Maso sauraronmu barkammu da wannan lokaci a cikin wani sabon shirinmu na sharhin al’amurran yau da kullum.

A yau mun sake kasancewa tare da Ferfesa Murat Yesiltas akan maudu'in dake sharhi akan dangantakar Turkiyya da Amurka.

Akwai muhimman abubuwa guda hudu game da hudan Turkiyya da Amurka. Idan ba a wareware wadanan abubuwan ba , da wuya huldan kasashen biyu ta yi wata tasiri. Daga cikin wadannan abubuwan rashin jituwan akwai maslahar S-400. Wannan dai ba lamari ne da zai haifar da da mai idanu ga kasashen biyu ba, bai kuma kamata ya zama wani abin da zai haifar da matsala tsakanin kasashe biyu ba, bai kuma kamata ya zama wani abin da Amurka zata tsangwami kawarta ta NATO ba. Ya dai kamata kasashen biyu su dauki matakai kwarara da zasu magance dukkanin matsalolin dake tsakaninsu. Bai kamata a dauki matakan kalubalantar juna tsakanin kasashen biyu ba.

Matakan da ministan harkokin tsaron kasar Turkiyya ya bayyana shi ne abin dubawa anan. Sai dai wannan matakin bai yi kamada wanda zai yi aiki ba. Akan hakan ne ake ganin cewa yunkurin siyar paket na biyu na makamin S-400 da kuma lamurran Girit zai iya kasancewa mai wuyar gaske. Bugu da kari, maslahar S-400 ba abu ne wanda Turkiyya zata yi watsi dashi ba, ba kuma abu ne wanda Amurkan zata kyale ba.

Maslahar kungiyar ta'addar YPG na daga cikin abubuwan da suke haifar da rashin jituwa tsakanin Turkiyya da Amurka. Ganin yadda kungiyar ta'addar YPG ke kara kai hare-haren kin kari a Arewacin Siriya da kuma irin yadda gwamnatin Biden ke kallon YPG dangantaka tsakanin kasashen biyu zai kara tsami. Hakan kuma lamari ne da zai kara kamarin maslahar S-400 tsakanin Turkiyya da Amurka lamarin da zai iya sanya Turkiyya daukar matakan soji. Dukkanin wadanan lamarin dake faruwa tsakanin Turkiyya da Amurka nada nasaba ne akan yadda Amurka ta ware wa Turkiyya a maslahar Siriya. A halin yanzu dai ko dai Amurka ta daina muamala da YPG ta yi hadin gwiwa da Turkiyya a Siriya ko kuma dai; Turkiyya ta dauki matakan kara kalubalantar YPG, lamarin da ake ganin cewa dukkanin kasashen biyu ko wace na zaben ta tsaya tsayin daka akan zabinta, bi ma'ana da wuya a samu jittuwa tsakanin kasashen biyu.

Duk da yake dai maslahohin S-400 da kungiyar ta'addar YPG suka kara tsamin dangantakar Turkiyya da Amurka; maslahar Gabashin Bahar Rum ta kasance wata ma'auni auna huldan kasashen biyu. A yayin da Turkiyya ke kallon maslahar Gabashin Bahar Rum a matsain lamurran tattalin arziki, siyasa da soji, Amurka na kallon lamarin a matsayin yunkurin mallakar iyaka. Akan hakan ne Amurka ke daukar matakan kara karfin sojin Girka domin ragewa Turkiyya karfi a yankin. Ankara na daukar matakan “ Blue Citizen” domin bin hanyar lumana ta yadda za’a iya kawo karshen maslahar yankin Gabashin Bahar Rum ama ga dukkan alamu wannan ba abu ne da za’a yi nasara akai ba. Sabili da haka maslahar Gabashin Bahar Rum zai iya kasancewa abinda zai iya kara dagule huldan kasashen biyu.

Kari da lamarin kungiyar ta’addar FETO, da kuma takunkumin da za’a kakkaba da kuma kara da za’a sanya, hadi da matsalolin da muka ambata a baya, babu shakkan cewa hulda tsakanin kasashen biyu na fuskanatar tangarda. Ganin irin yadda sifar matsalolin suke, da wuya a iya bayyana cewa za’a iya kawo karshensu cikin dan kankanen lokaci.  La'akari da cewa wasikar da sanatoci 54 suka rubuta ta kasancene akan hukunntawa da kalubalantar Shugaba Erdoga maimakon son gyarar alakar Turkiyya da Amurka ba zai yiwu a bayyana cewa za’a iya samun sulhu daga majalisar ba. Gwamnatin Biden da ta bayyana cewa za ta dora tsarin harkokin wajenta ne tare da yin hulda da ma’aikatu da kuma irin yadda ministan harkokin wajen Amurka Blinken ke kasancewa tare da majalisa matakan da zasu dauka akan wasu kasashe kamar Turkiyya zai iya banbanta daga yadda ake tunani

Idan muka dubi tsarin harkokin waje ta amfani da majalisar Turkiyya da idon basiri, da kuma irin tsarin harkokin wajen Amurka dake akan kasa da kasa, harkokin Turkiyya ka iya kara wahala kwarai da gaske, haka kuma hulda tsakanin Turkiyya da Amurka a karshe dai lamari ne da za’a bari a zauren majalisa.

 Labarai masu alaka