Erdoğan ya karbi sabbin jakadun Ivory Coast, Saliyo da na Polan a Turkiyya

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, ya karbi sabbin jakadun kasashen Ivory Coast Khadidjata Toure, na Polan Jakub Kumoch da kuma na Sierra Leone Muhammed Hassan Kai-Samba

1455016
Erdoğan ya karbi sabbin jakadun Ivory Coast, Saliyo da na Polan a Turkiyya

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, ya karbi sabbin jakadun kasashen Ivory Coast Khadidjata Toure, na Polan Jakub Kumoch da kuma na Sierra Leone Muhammed Hassan Kai-Samba a matsayinsu na sabbin nadaddun jakadun kasashensu a Turkiyya.

A bikin da aka gudanar a Ankara babban birnin Turkiyya jakadun sun mikawa shugaba Erdogan takardar gasgantawarsu dake tabbatar da zasu fara aiki a matsayin jakadun kasashensu a Turkiyya.

Bayan gabatar da takardun tabbacin nasu shugabanin sun dauki hotuna domin kafa tarihi.

 Labarai masu alaka