Guterres ya tattauna da Sarraj ta wayar tarho

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya tattauna ta wayar tarho da Firaministan Libiya Fayyaz Al-Sarraj.

1447260
Guterres ya tattauna da Sarraj ta wayar tarho

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya tattauna ta wayar tarho da Firaministan Libiya Fayyaz Al-Sarraj.

Sanarwar da aka fitar daga ofishin yada labarai na Majalisar ta ce a yayin tattaunawar, Sarraj ya sake jaddada alkawarinsu na kawo sauyin siyasa a Libiya, warware rikicin kasar da kuma batun gudanar da zabe.

Sanarwar ta ce Shugabannin 2 sun kuma tattauna kan ya kamata a sake bude rijiyoyin man fetur na Libiya da aka rufe, kuma Guterres ya bayana bakin cikinsa game da kaburburan da aka samu an binne mutane da dama a cikinsu a yankin Terhune na Libiya, sannan a shirye suke da su taimakawa kasar don yaki da anobar Corona (Covid-19).

Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric, a yayin taron manema labarai da yake gudanarwa a kowacce rana ya bayyana cewar Guterres ya kuma tattauna ta wayar tarho da dan tawaye kuma dan juyin mulki Haftar Khalifa da ke gabashin Libiya.Labarai masu alaka