An saukaka dokar cin zabe a Kirghizistan

A kasar Kirghizistan an rage yawan kason kuri'u da mai neman takarar dan majalisa ya kamata ya samu kafin a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe daga kaso 9 cikin dari zuwa 7

1446747
An saukaka dokar cin zabe a Kirghizistan

A kasar Kirghizistan an rage yawan kason kuri'u da mai neman takarar dan majalisa ya kamata ya samu kafin a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe daga kaso 9 cikin dari zuwa 7.

Shugaban kasar Kirghizistan Sooronbay Ceenbekov, ya rataba hannu akan dokar da ta amince da rage kason kuri'an da dan majalisa zai samu kafin ya kasance zabebbe daga kashi 9 zuwa 7 cikin dari.

Dangane ga bayanan da suka fito daga ma'aikatar sadarwa fadar shugaban kasa shugaba Ceenbekov ya rataba hannu akan dokar sauye ka'idodin zaben 'yan majalisu a kasar.

Wannan dokar ta fara aiki ne daga ranar 18 ga watan Yuni.

A kasar Kirghizistan da ake zaben 'yan majalisu sau daya cikin shekaru biyar za'a gudanar da zaben mai zuwa ne a ranar 4 ga watan Oktoba.

 Labarai masu alaka