Erdogan: Za mu ci gaba da yin duk mai yiwuwa don dawo da zaman lafiyar Siriya

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewar "Za mu ci ga da yin duk duk mai yiwuwa don ganin nan da nan Siriya ta samu zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali."

1447123
Erdogan: Za mu ci gaba da yin duk mai yiwuwa don dawo da zaman lafiyar Siriya
ASTANA 1.jpg

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewar "Za mu ci ga da yin duk duk mai yiwuwa don ganin nan da nan Siriya ta samu zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali."

Shugaba Erdogan ya halarci taro kwatankwacin na Astana ta hanyar sadarwar bidiyo tare da Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin da Shugaban Iran Hasan Ruhani inda suka tattauna kan Siriya.

A jawabin da Shugaba Erdogan ya yi ya ce "Tun farkon fara rikicin, Turkiyya ta kasance tare da 'yan uwanta jama'ar Siriya. Ba tare da kallon kabila, addini, asali ko sura ba mun rungumi 'yan kasar Siriya."

Shugaba Erdogan ya ce sun nuna damuwa matuka don ganin ba a yi amfani da ta'addanci ba wajen rarraba kasar Siriya.

Ya ce "Ta hanyar amfani da karfin soji da magance matsalolin masu neman mafaka mun sha gaban 'yan a ware. "Za mu ci ga da yin duk duk mai yiwuwa don ganin nan da nan Siriya ta samu zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali. A matsayinmu na garanton Astana, hadin kanmu ne zai bayyana makomar kasar."

Bayan jawabin na Erdogan, an gudanar da taro tsakanin Turkiyya, Rasha da Iran.

Bayan taron shugabannin kasashen sun fitar da sanarwar hadin gwiwa.Labarai masu alaka