An kwayewa Shugaban Kasar Faransa Macron baya

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron da jam'iyyarsa ta LREM sun sha babban kayi a zagaye na 2 na kananan zabukan da aka gudanar a kasar.

1445046
An kwayewa Shugaban Kasar Faransa Macron baya

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron da jam'iyyarsa ta LREM sun sha babban kayi a zagaye na 2 na kananan zabukan da aka gudanar a kasar.

A daren Lahadin nan aka gudanar da zabukan wadanda aka shirya yi a watan Maris amma sakamakon annobar Corona (Covid-19) aka dage zuwa watan Yuni.

An bayyana cewar mutane miliyan 16 wato kaso 60 na masu jefa kuri'a ne ba su fita zaben ba wanda hakan ya kafa tarihi. A shekarar 2014 adadin na a kaso 34,87.

Kuri'un da aka kirga sun nuna jam'iyyar LREM ta sha kayi a manyan birane kamar yadda ta afku a zagayen farko na zaben. Jam'iyyar EELV kuma ta lashe zabe a garuruwan Lyon, Bordeaux, Strasbourg, Poitiers, Besanchon da Marselle.

Firaminista Edouard Philippe ya samu nasara da kaso 58,83 cikin dari a zaben da ya shiga a Le Havre.

Shugabar Birnin Paris 'yar jam'iyyar PS Anne Hidalgo ta sake lashe kujerarta da kaso 48,7 inda ta samu damar yin tazarce.

A Perpignan kuma jam'iyyar RN ta Marine Le Pen ta yi nasara da kaso 52 na kuri'un da aka jefa inda dan takararta Louis Aliot ya zama magajin gari.Labarai masu alaka