Falasdin ta sanar da kawo karshen musayar bayanai da CIA

Sakamakon wata yarjejeniya da Isra'ila da Amurka suka sanya hannu a kai wadda Falasdin ba ta ciki, kasar ta Falasdin ta ce za ta kawo karshen musayar bayanai da Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA).

1421436

Sakataren Majalisar Gudanarwar Kungiyar 'Yantar da Falasdinawa Said Uraykat ya bayyana cewar domin mayar da martani ga mamayar yankunan Falasdinawa da Isra'ila ke yi ba bisa ka'ida ba, Hukumar Leken Asiri ta Falasdin za ta kawo karshen yin musayar bayanai da Amurka.

Uraykat ya ce "Awanni 48 da suka gabata mun sanar da mahukuntan CIA cewar yarjejeniyar da muka kulla da su ta daina aiki. Babu sauran hadin kanmu da Amurka ko ısra'ila ta bangaren tsaro."Labarai masu alaka